Wata kotu a jihar Kano, ta yanke wa wani matashi ɗan Tiktok, mai suna Umar Hashim Tsulange hukuncin ɗaurin shekara guda saboda samunsa da laifin taka doka.
Shafin Freedom Radio a jihar ya ruwaito cewa kotun ta ba shi zaɓin zaman gidan yari ko biyan tarar naira 80,000.
Umar Tsulange ya yi fice shafin Tiktok inda a wasu lokutan ake ganinsa yana wanka ko kwanciya ko wani abu da zai ɗauki hankalin jama’a a tsakiyar titi gaban ababen hawa da danja ta tsayar.
Kazalika kotun ta umarci Tsulangen ya biya Hukumar Tace Fina-finai diyyar Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi na gurfanar da shi.
A watannin da suka gabata ne rundunar ƴansandan jihar Kano ta ja hankalin matasan da ke tsayawa tsakiyar titi domin ɗaukar bidiyo, tana mai cewa hakan na haifar da hatsura a wasu lokuta.