Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas, ta samu watai likita, Anuoluwapo Adepoju, tare da yanke mata hukunci bisa samunta da laifin yin wata tiyatar sauya halita waddda ta yi sanadin mutuwar wata mata mai suna Nneka Onwuzuligbo a shekarar 2020.
Mai shari’a Mohammed Liman ya same ta da laifi, kuma ya yanke mata hukuncin daurin shekara daya a gidan yari.
Sai dai an ba ta zabin biyan tarar Naira dubu 100,000 a madadin zaman gidan yari.