An yankewa wani dan kasar Lebanon mai suna Zuhier R Akar mai shekaru 67 hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata da wasu ‘yan mata biyu a Kano.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, karkashin mai shari’a S. M Shuaibu, ta yanke wa Akar hukuncin a ranar Laraba.
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen jihar Kano ta gurfanar da Akar a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na safarar mutane da kuma lalata da su.
Mai shari’a S M Shu’aibu ya samu Akar da laifi, inda ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba amma ya umarce shi da ya biya Naira miliyan 2 domin jinyar wadanda lamarin ya shafa.
A cewar mai gabatar da kara, karkashin jagorancin kwamandan shiyyar Kano Abdullahi Babale, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kai karar hukumar NAPTIP a ranar 5 ga Satumba, 2024.
Akar dai ya sayo ‘yan matan masu shekaru 14 da 15 a kusa da Suya Spot kuma ya yi lalata da su a gidansa. Daga baya aka yada hoton bidiyon lamarin a shafukan sada zumunta.
Masu gabatar da kara sun gabatar da nune-nune hudu, ciki har da ikirari na Akar da kuma shaidar wadanda abin ya shafa, don tabbatar da karar su.
Akar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya saba wa dokar tilastawa da gudanar da fataucin mutane (Haramta) ta 2015.
Lauyan tsaro R A Kasali ya roki a yi masa sassauci a madadin Akar.