Wata kotu a garin Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani dalibi mai suna David Longji mai shekaru 23 hukuncin daurin watanni uku a gidan yari bisa samunsa da laifin satar na’urar sarrafa hasken rana.
Alkalin kotun, Mista Shawomi Bokkos, ya yanke wa Longji hukunci bayan ya amsa laifin sata.
Sai dai Bokkos ya ba shi damar biyan N20,000 a matsayin tarar.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insp Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 16 ga watan Oktoba a ofishin ‘yan sanda na Anglo-Jos da wani Livinus James, wanda ya shigar da kara.
Lauyan mai gabatar da kara ya ce wanda ake tuhumar ya saci na’urar hasken rana daga wani kamfani kuma an kama shi ne a lokacin da yake kokarin sayar da ita.
Gokwat ya ce laifin ya saba wa tanadin kundin hukunta manyan laifuka na Filato.


