A ranar Laraba ne wata kotun karamar hukumar Karu da ke Abuja, ta bayar da umarnin a tsare wasu leburori biyu a gidan gyaran hali, bisa zarginsu da satar igiyoyi masu sulke na wutar lantarki.
‘Yan sandan sun tuhumi Nature Mark mai shekaru 27 da Gabriel Sebastian mai shekaru 22, da laifin hada baki, barna da kuma sata.
Alkalin kotun, Mista Hassan Mohammed, ya dage bayar da belin wadanda ake kara sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Disamba domin sauraren karar.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali na Keffi a jihar Nasarawa har sai an kammala binciken da ‘yan sanda za su gudanar.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Mista Olanrewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa, babban jami’in tsaro na kamfanin gine-gine na ENL da ke Guzape, Abuja ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Asokoro.
Osho ya shaida wa kotun cewa a ranar 8 ga watan Nuwamba, an kama wadanda ake tuhuma da igiyoyin sulke na kamfanin.
Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 97, 327 da 288 na penal code.
Wadanda ake tuhumar dai sun musanta aikata laifin.