A ranar Laraba ne wata kotu da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato, ta yanke wa John Shedrack, mai shekaru 26, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar kaji 100 da darajarsu ta kai N300,000.
Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.
Bokkos ya baiwa mai laifin zabin biyan tarar Naira 20,000 ko zaman gidan yari na watanni uku sannan kuma ya bukaci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya diyya N300,000 ga wanda ya kai karar ko kuma a daure shi na watanni shida a gidan yari.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insp Monday Dabit, ya shaida wa kotun cewa Mista Ikechukwu Egwuonwu ne ya kai karar a ofishin ‘yan sanda na Rantya a ranar 19 ga watan Yuni.
Ya ce wanda ake zargin ya kutsa kai cikin gonar kiwon kajin mai korafin kuma ya sace masa kajin.
Dan sanda mai gabatar da kara ya ci gaba da shaida wa kotun cewa a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin.
Laifin a cewarsa ya sabawa dokar jihar Filato ta Arewacin Najeriya.


