Kotu da dakatar da wa’adin da Najeriya ta bai wai kamfanin Meta, mallakin Facebook da Instagram da WhatsApp, na biyan tarar dala miliyan 290 bayan da kamfanin ya shigar da ƙorafi a kotu, wanda hakan ya dakatar da wa’adin biyan tarar.
Tun da farko, hukumar sanya ido kan gogayya tsakanin kamfanoni da kuma kare haƙƙin masu sayen kayayyaki (FCCPC) ta sanya wa Meta wa’adin 30 ga Yuni, 2025, domin biyan tarar da aka kakaba masa bayan samun shi da laifin taka dokokin da suka jiɓanci gasa da tallan haja da kuma na bayanan sirri.
Sai dai FCCPC ta tabbatar wa BBC cewa Meta ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin a kotun daukaka ƙara.
Kamfanin Meta ya kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin har zuwa lokacin da kotu za ta yanke shawara.
A watan Mayu ne kamfanin na Meta mamallakin Facebook ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya bisa abin da ya bayyana da tarar da ta wuce hankali.
Wani rahoto ya nuna cewa al’ummar Najeriya ka iya rasa damar ci gaba da hulɗa da shafukan Facebook da Instagram idan dai har kamfanin na Meta ya aiwatar da barazanar da ya yi na rufe ayyukan nasa a ƙasar.