Babbar kotun tarayya ta ɗage shari’ar da take yi wa jagoran fafutikar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu kan alaƙa da ta’addanci da gwamnatin tarayya ke zarginsa da shi.
Mai shari’a Binta Nyako ta ce ta ɗage shari’ar ne har zuwa lokacin da za a yanke hukunci game da ɗaukaka ƙarar da gwamnatin tarayya ta yi kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 13 ga watan Oktoba, wadda ta wanke shi daga zarge-zargen alaƙa da ta’addanci.
Gwamnatin tarayya ta ɗaukaka ƙara ne a gaban kotun ƙolin ƙasar tana mai neman kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka ƙarar.
Nnamdi Kanu dai bai halarci zaman kotun na ranar Litinin ba.