Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar yaƙi da cinhanci ta EFCC ta shigar kan tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Afrilu ne bayan lauyan EFCC, Kemi Phinro, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman ba saboda “wani wanda yake da kariya na ba shi mafaka”, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.
Lauyan ya ƙara da cewa hukumar na duba yiwuwar haɗa kai da dakarun soja don ganin sun kama tsohon gwamnan.
Tun a jiya Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya a motarsa lokacin da jami’an hukumar suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.
EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.