Wani kwamiti mai mutum uku na Kotun Kare masu saye da sayarwa, ya umarci Multichoice Nigeria da ta bai wa masu kallon talabijin din DSTV da GOtv wata guda a matsayin kyauta.
Kotun ta kuma ci tarar Multichoice naira miliyan 150 saboda kalubalantar hurumin kotun, wanda a kwanakin baya ta hana ta kara farashin katin DSTV da GOtv.
Mai shari’a Thomas Okosu ne ya bayar da wannan hukunci a ranar Juma’a a Abuja.
A watan Mayu, Multichoice Nigeria ta kara farashin biyan kuÉ—i na fakitin DStv da GOtv duk da umarnin kotun.
Kotun ta dakatar da kamfanin Multichoice Nigeria Limited daga kara kudin kati da kuma farashin da ta ke shirin farawa a ranar 1 ga watan Mayu.