fidelitybank

Kotu ta ce a rataye wanda ya kashe Dan Acahaba a Legas

Date:

Mai shari’a Olukayode Ogundana na babbar kotun jihar Ekiti, ta yankewa wani Ajakaiye Toyin hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe wani dan kasuwa mai suna Afe Omonyi, direban babur (Direban Okada) a ranar 23/08/2018 akan titin Agbado/Ode Ekiti.

Bayanai na kotun sun ce direban Okada ya kai mai laifin ne daga Agbado-Ekiti a ranar kaddara zuwa gonarsa da ke kan titin Ode-Ekiti kan kudin sufurin da aka amince da shi na Naira 150.00.

Da ya isa gonar, wanda aka yankewa laifin ya baiwa mutumin Okada Naira 200.00, sannan ya bukaci a canza masa N100.00 wanda dan Okada din ya ki amincewa ya bashi canjin Naira 50.00.

Daga nan ne aka yi gumurzu, sai wanda aka yanke wa hukuncin ya shake shi har lahira ta hanyar daure masa igiya a wuyansa, ya kuma tona wani kabari mara zurfi ya binne shi.

Daraktan kararrakin jama’a, Julius Ajibare, wanda ya shigar da kara a jihar, ya kira shaidu 4 tare da gabatar da shaidu 7 don tabbatar da karar ba tare da wata shakka ba.

Omoniyi Idowu ya wakilci wanda aka yankewa hukuncin.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...

Gwamnati za ta gina titin jirgi a jihohi shida

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da...

Tinubu ya na cikin koshin lafiya – Farouk Adamu Aliyu

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu...

Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar a kamo jagoran ‘yandaban Haiti

Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada...

Gwamnati ta janye karar da ta shigar kan Fasinjar jirgin Ibom

Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan...

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...
X whatsapp