Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke Uyo ta yanke wa Uduak Frank Akpan, wanda ake zargi na farko da laifin kashe Iniubong Umoren hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A cikin hukuncin sama da sa’o’i biyu da alkalin kotun, Bassey Nkanang ya yi, an samu wanda ake tuhuma da laifin fyade da kisa.
Kotun ta yanke masa hukuncin rataya a wuyansa har sai ya mutu.


