Babbar kotun jihar Osun da ke zamanta a Osogbo, ta yanke wa Dr Raheem Adedoyin hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Timothy Adegoke.
Da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Talata, babban alkalin jihar Osun, Mai shari’a Adepele Ojo, ya kuma yanke hukuncin kisa ga wasu ma’aikatan otal din Hilton, Ile-Ife, Adeniyi Aderogba da Kazeem Oyetunde.
Timothy Adegoke dalibin digiri ne na biyu a Jami’ar Obafemi Awolowo, OAU, Ile-Ife, wanda ya rasu a watan Nuwamba, 2021 a Hilton Hotels, Ile-Ife, Jihar Osun.
Kotu ta sallami ma’aikatan Otal din Hilton uku, Ile-Ife, Magdalene Chiefuna, Lawrence Oluwole da Adedeji Adesola, inda kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wanda ake tuhuma na bakwai a ranar Laraba.


