Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, ta bukaci jam’iyyar PDP da ta yi nazari mai zurfi kan ci gaban da ta samu a cikin karar ta don sanin ko za ta iya ci gaba da shari’ar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da wannan shawarar ne bayan lauyan jam’iyyar PDP, Joseph Daudu, SAN, ya shaida wa kotun cewa, bisa hukuncin kotun daukaka kara da ke Abuja, FHC na iya ci gaba da shari’ar da ke gabanta.
Kamfanin dillancin labaran na kasa (NAN) ya rawaito cewa, jam’iyyar PDP ta maka shugaban kasa, babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da kuma magatakardar majalisar dokoki ta kasa.