Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani Hakimin Kauye mai suna Efen Ibom, karamar Hukumar Ika, mai shekaru 82, mai suna Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan kai.
Wanda aka yanke wa hukuncin, yana auren mata 12 da ‘ya’ya 60, yana fuskantar shari’a, bisa wasu tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da hada baki, da jagorantar shari’ar da ba ta dace ba ta hanyar gwaji, satar babur da kuma kashe mai gida, dan unguwarsu, Udoma Akpan Udo Ubom. .
A hukuncin da kotun ta yanke a karkashin mai shari’a Edem Akpan, ta samu wanda ake zargin da laifin kashe Udoma Akpan Udo Ubom ta hanyar zuba masa wani sinadarin wanda ya kai ga mutuwarsa a ranar 26 ga Afrilu, 2017.
‘Yan uwansa sun tuhumi marigayi Ubom da cewa matsafi ne, inda suka kai rahoto ga Hakimin Kauyen, wanda ya kai shi gaban Majalisar Efen, inda aka yi wa marigayin rantsuwa cewa shi ba mayen ba ne.


