Kotu a Koriya ta Kudu ta bayar da sammancin kama Shugaban Ƙasa Yoon Suk Yeol, wanda majalisa ta tsige da dakatar da shi sakamakon kokarin da ya yi na sanya dokar soji a ƙasar.
Masu bincike sun buƙaci a bayar da sammanci ne bayan ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa domin amsa tambayoyi.
Ba a faɗi lokacin da za a kamo shi ba, sai dai wakilin BBC a birnin Seoul ya ce ana fatan wannan barazana ta iya tilasta wa Mista Yoon gabatar da kansa.
Wasu ‘yan kasar na ta tsokacin cewa tuntuni ya kamata a kama shugaban bayan ya ayyana batun kafa dokar soji.
Lauyansa dai ya ce sammacin kama shugaban ya saba doka da ‘yancinsa na ɗan’adam.