fidelitybank

Kotu ta bayar da izini a kashe ‘yan Bijilante 5 a Kano

Date:

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa wasu `yan banga biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta kama su da laifin kisan wani matashi mai shekara 17.

‘Yan bangar sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun 2022.

‘Yan bangar, waɗanda suke aiki a cibiyar bunƙasa rayuwar matasa ta Sani Abacha da ke kan hanyar Madobi, sun haɗa da Emmanuel Korau da Elisha Ayuba da Irimiya Timothy da Auwalu Jafar da kuma Mustapha Haladu.

Lauyan da ya gabatar da kara Barrister Lamido Soron Dinki, gabannin yanke hukuncin ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargi sun kama matashin ne a sabon titi, Panshekara, inda suka far masa da duka da da sanduna, kana daga bisani suka raunata shi ta hanyar caka masa wuka, kana suka ja shi a kasa suka jefa shi cikin keken a daidaita sahu, lamarin da ya yai sanadin mutuwarsa.

Lauyan waɗanda aka yi ƙarar ya yi ƙokarin kare su, inda ya bayyana cewa sun je ne da nufin kama matashin ba halaka shi ba, bayan an kai musu karan sa.

Sai dai, kamar yadda mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Malam Baba Jibo Ibrahim ya ce, mai shara`a Dije Aboki ta yanke wa `yan bangan hukunci ne bayan ta gamsu da hujjojin da mai gabatar da ƙarar ya gabatar:

Sai dai kuma mutanen da aka yanke wa hukuncin na da damar ɗaukaka ƙara.

news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp