Kotun ɗa’ar ma’aikata ta bayar da belin shugaban hukumar karbar ƙorafi da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Kotun – wadda ke zamanta a Abuja – ta ba da belin Muhuyi ne bisa sharaɗin ajiye naira miliyan biyar tare da mutum biyu mazauna Abuja da za su tsaya masa, sannan su nuna shaidarsu ta kwakkwaran aikin da suke yi, kuma su bayyana shaidar karfin samunsu.
Dole ne kuma masu tsaya wa Muhyi Rimin Gado su gabatar da ƙananan hotunansu da na wanda suke tsayawan.
Haka kuma kotun ta ce dole ne Muhuyi ya gabatar takardar shaida daga wani fitaccen mutum mazaunin Abuja da ke aiki ko sana’a a babban irnin.