Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye kan kuɗi naira miliyan 50.
Da yake yanke hukunci a yau Alhamis, mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun, ya buƙaci tsohon ministan da ya gabatar da mutane biyu waɗanda za su tsaya masa
An gurfanar da Agunloye ne a gaban kotu ranar Laraba, bisa zargin almundanar kuɗi da ya kai dala biliyan shida a badaƙalar kwangilar wutar Mambila.
Mai shari’ar ya ce dole ne mutanen su kasance masu hannu da shuni waɗanda kuma ke zaune a Abuja.
Ya ce tilas ne kuma su mallaki kadarorin da ya kai Naira miliyan 300 tare da takardar shaidar zama wanda za a iya tantancewa.
“Dole ne kuma su miƙa kwafin katin shaidarsu da kwafin fasfo ɗin su na ƙasashen waje ga kotu,” in ji Onwuegbuzie.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Febrairu.