Babbar kotun tarayya da ke brnin Ilorin a jihar Kwara ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Abdulfattah Ahmed kan kudi naira miliyan 50 tare da sharadin mutum biyu da za su tsaya masa wadanda suka mallaki fili a birnin Ilorin.
Haka kuma cikin sharadin belin tsohon gwamnan zai ajiye fasfo dinsa na tafiye-tafiye da sauran sharuda.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a ranar Juma’a, biyo bayan gayyatar da hukumar ta yi masa domin amsa tambayoyi a ranar Litinin.
Sai dai kuma an hana ‘yan jarida shiga kotun.
Hukumar EFCC ta kama Ahmed a ranar Litinin inda ake yi masa tambayoyi kan hada-hadar biliyoyin naira a lokacin da yake gwamnan jihar.
Ahmed ya kasance gwamnan jihar Kwara tsakanin watan Mayun 2011 zuwa Mayu 2019 kafin ya mikawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
An taba yi masa tambayoyi a watan Mayun 2021 a hedikwatar EFCC da ke unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, kan zargin karkatar da kuÉ—ade kusan Naira biliyan 9 daga asusun jihar.


 

 
 