Kotun Majistare ta Kano, ta bayar da belin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimingado da aka dakatar.
A ranar Juma’a ne aka gurfanar da Muhuyi Magaji Rimingado a gaban kotu, bisa laifin bayar da bayanan karya da ‘yan sanda suka yi.
Solacebase ta ruwaito cewa, babban alkalin kotun, Aminu Gabari ya bayar da belin wanda ake kara akan kudi Naira 500,000 tare da tsayayyu biyu da suka hada da uwa ko uba na wanda ake kara da kuma babban limamin masallacin juma’a na Sharada ko Ja’en.