Mai sharia’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Alƙalin ya bayar da umarnin sakin Emefiele nan take ga lauyoyinsa, waɗanda aka ɗora wa alhakin kai shi kotu a zaman da za a yi a makon gobe da kuma duk lokacin da ake buƙata.
Alƙalin ya kuma ce wajibi ne ga tsohon shugaban bankin na CBN ya ajiye dukkanin takardun tafiye-tafiyensa a hannun magatakardar kotun kafin shari’ar ta kankama.
Haka nan ta kuma ce dole ne a daina tsare shi ba tare da shari’a ba.
Kotun ta ce ba za ta kawar da idonta daga batun cewa ya shafe kwana 151 a tsare ba, kuma kotun ta ce dole ne gwamnatin tarayya da ministan shari’a su martaba umarnin kotu.


