fidelitybank

Kotu ta bayar da belin Dan Sarauniya akan wasu sharuda

Date:

Kotun Jihar Kano ta bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya.

Kotun mai lamba 58 da ke zamanta a unguwar Nomansland, ta bayar da belin ne kan Naira miliyan daya, tare da gindaya masa wasu sharuda da sai ya cika belin za ta sake shi.

Mai shari’a Aminu Gabari ya ce, bayan biyan kudin da Dan Sarauniya zai yi sai ya kuma ajiye fasfo dinsa na tafiya.

Kazalika zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa, dole na farko ya zama mai garin kauyen Sarauniya wato kauyen da ya fito, na biyun kuma dole ya zama limamin garinsu ko kuma kwamandan Hizban garin.

A ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama Injiniya Mu’azu a Abuja babban birnin Najeriya.

An kuma mayar da shi jihar Kano inda ‘yan sanda suka gabatar masa da tuhume-tuhumen da ake zarginsa da su, na keta mutunci gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje.

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp