Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, ta bayar da belin dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Fatakwal 2, a majalisar dokokin kasar Chinyere Igwe, a kan kudi N100,000.
Alkalin kotun, Mai shari’a Stephen Daylop-Pam, a hukuncin da ya yanke kan neman belin, ya umurci Igwe ya mika fasfo dinsa na kasa da kasa ga hukumar shige da fice ta Najeriya.
An dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 4 ga Mayu, 2023.
Rundunar ‘yan sandan ta kama Igwe ne bayan da ta gano cewa yana hannun sa dala 498,000 a ranar 24 ga watan Fabrairun 2023, yayin wani samame da ‘yan sandan suka kai masa. An tuhume shi da laifin karkatar da kudade.