A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta baiwa tsohon gwamnan jihar Imo, Anayo Rochas Okorocha, izinin tafiya kasar Burtaniya domin neman lafiya.
Mai shari’a Inyang Eden Ekwo, wanda ya ba da izinin, ya umarci magatakardar kotun da ya ba shi fasfo din tafiya na tsohon gwamnan domin gudanar da ziyarar jinya.
Umurnin alkalin ya biyo bayan bukatar da wani babban Lauyan Najeriya, Mista Ola Olanipekun ya yi, wanda ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa na fama da matsalar lafiya a ‘yan kwanakin nan.
Babban Lauyan ya bayyana cewa, Okorocha, wanda yanzu Sanata ne mai wakiltar Imo ta Arewa a Majalisar Dattawa, ba zai yi amfani da wannan umarni ba, kuma zai dawo kasar domin yi masa shari’a.
Ko da yake, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, wanda Mista Chile Okoroma ya wakilta ya nemi yin kakkausar suka da wannan bukata, hukumar ta tausasa murya lokacin da Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewa za a amince da bukatar tare da gargadin kotu.
Yayin da yake amsa wannan bukata, Mai shari’a Ekwo ya umarci Okorocha da ya mayarwa magatakardar kotun fasfo din kasa da kwanaki uku da isowarsa kasar.
Alkalin kotun ya ce zai bayyana Okorocha na nemansa idan ya yi yunkurin yin amfani da damar da aka yi masa.
Daga nan ne mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 7 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’ar sa kan tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta gabatar masa.