Kotun ƙoli ta umarci gwamnonin jihohin kasar nan 36, da su kare kansu cikin kwanaki bakwai, kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman cikkaken ‘yancin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774.
A zaman kotun na yau alakalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Garba Lawal, kotun ta bai wa gwamnonin jihohi 36 umurnin shigar da bayanan kare kansu a gabanta a cikin kwanaki bakwai daga yau.
Alƙalan sun bai wa babban lauya, Lateef Fagbemi umurnin bayyana martaninsa da ke nuna matsayar gwamanati a cikin kwana biyu da shigar da nasu ƙorafin kariya.
A karar da gwamnatin tarayyar ta shigar ta hannun babban lauyanta Lateef Fagbemi ya kuma nemi kotun ta bayar da damar da za a iya tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu daga asusun gwamnatin tarayya kai tsaye, kamar yadda ƙundin tsarin mulkin kasa ya bayar.
Babban lauyan ya kuma ce yin wani abu saɓanin hakan daidai ya ke da karya dokokin ƙasa da ƙundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya bayar da dama.
Gwamnatin tarayyar ta kuma roƙi kotun ƙolin ta yi la’akari da sashe na ɗaya da na huɗu da na biyar waɗanda suka tilasta wa gwamnonin da ‘yan majalisar dokokin jihohi su tabbatar da cikakken tsarin dimokradiyya a mataki na ƙasa ba wai kama karya ba irin yadda ake yi a yanzu.
Kotun ƙolin ta ce dole ne a kammala gabatar da dukkan matakai da musayar bayanai da suka kamata a kan lokaci, inda ta sanya ranar 13 ga watan Yuni don sauraron bayanan ƙarar da gwamnonin za su shigar.
Gwamnonin jihohin na ci gaba da iko da kusan komai na ƙananan hukumomi 774 a kasar nan.