Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da karar da ke neman tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta binciki zargin alakanta Karamin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle da zargin tallafawa ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.
Karamin wanda dan rajin kare hakkin bil’adama, Abubakar Dahiru ya kawo, na da nufin gudanar da bincike kan zargin da Matawalle ya yi na hannu a ayyukan ‘yan bindiga a lokacin da yake gwamna.
Takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1434/2024, ta bayyana shugaban kasa Bola Tinubu, da babban lauyan gwamnatin tarayya, da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) a matsayin wadanda ake kara na 1, 2, da na 3, bi da bi.
Dahiru, wanda lauyansa Ojonimi Apeh ya wakilta, yana rokon kotun da ta bayyana cewa dole ne shugaba Tinubu ya umurci IGP ya binciki ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara, tare da mayar da hankali musamman kan zarge-zargen da Matawalle ke takawa a rikicin.
Mai shigar da karar ya ce a lokacin Matawalle yana gwamna (2019-2023), ‘yan fashi da makami sun ta’azzara zuwa matakin da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya sa dubban al’ummar jihar Zamfara suka rasa matsugunansu, ko marayu, ko kuma zawarawa saboda tashin hankalin.
Dahiru ya yi nuni da hirarraki da kasidu da ke zargin Matawalle da goyon bayan ‘yan fashi, ciki har da ikirarin cewa ya bai wa ‘yan bindigar motoci, da yin zagon kasa ga kokarin tabbatar da doka da oda, da yin afuwa ga ‘yan ta’adda.
Dahiru ya kara da cewa, duk da wadannan munanan zarge-zarge, gwamnati ba ta yi wani yunkuri na binciken Matawalle ba, yayin da ‘yan fashi ke ci gaba da addabar jihar Zamfara. In ji Daily Post.


