fidelitybank

Kotu ta baiwa Atiku da Obi damar duba kayan zabe

Date:

Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bai wa ɗan takarar shugaban kasa a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Labour, Peter Obi damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

Tun farko ƴan takarar ne daban-daban suka miƙa buƙatar neman a ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a babban zaɓen 2023 tare da tilasta wa INEC ta ba su damar ganin kayan aikin da aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasar.

A ranar Laraba 1 ga watan Maris ne Atiku Abubakar ya shigar da tasa ƙarar yayin da Peter Obi kuma ya shigar da tasa ranar Alhamis biyu ga watan.

Kan haka ne kotun ta umarci hukumar zaɓe ta bai wa ɗan takarar PDP damar duba kayayyakin zaɓen.

A yau Juma’a kuma kotun ta amsa bukatun ‘yan takarar na duba kayan zaɓen sannan kuma su titsiye hukumar zaɓe kan wasu bayanai da za su buƙata.

Kotun ƙarƙashin mai shari’a Joseph Ikyegh ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari wasu ƙararraki da ƴan takarar biyu suka shigar tare da jam’iyyunsu.

PDP da LP waɗanda a baya-bayan nan suka yi watsi da sakamakon zaɓen, sun ce samun damar ganin kayayyakin za ta taimaka musu a ƙalubalantar sakamakon zaɓen da suke yi wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.

A cewar INEC, Tinubu ya ci zaɓen ne da ƙuri’u 8,794,726 inda Atiku Abubakar na PDP yake bi masa da ƙuri’u 6,984,520 sai Obi na Labour Party da ya zo na uku da ƙuri’u 6,101,533.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp