fidelitybank

Kotu ta baiwa APC kujerar majalisar tarayya a Katsina

Date:

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen ‘yan majalisar tarayya a jihar Katsina, ta soke zaɓen Dalha Ismail Kusada a matsayin ɗan majalisar wakilai.

A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a O. Ogunfowora ta ce Abubakar Yahaya Kusada na APC ne ya lashe zaɓen na watan Fabrairu.

Haka nan, alƙalan sun ayyana Abubakar a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Kankia/Ingawa/Kusada.

Kazalika, kotun ta umarci Dalha da hukumar zaɓe ta Inec  waɗanda ake ƙara su biya Abubakar kuɗi naira 200,000.

Da ma Abubakar ne ke riƙe da kujerar kafin Inec ta sanar da kayen da ya sha jim kaɗan kammala zaɓen, kuma tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

Sai dai har yanzu Dalha Kusada na da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp