Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar NDLEA na neman izinin ci gaba da tsare Abba Kyari da wasu mutum shida da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta bayar da umarnin a tsare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus na tsawon kwanaki 14 a cibiyar NDLEA da ke Abuja kafin a gudanar da bincike
Mai shari’a Zainab Abubakar ta ba da wannan umarni ne bayan ta saurari shugaban lauyoyin NDLEA, Joseph Sunday wanda ya nemi a ci gaba da ajiye mutanen.
Hakazalika, kotun ta ce hukumar na da ‘yancin sake neman karin wa’adin tsare wadanda ake zargin, bayan cikar wa’adin kwanaki 14.