Babban Kotun Majistare da ke Makurdi a jihar Benue, a ranar Juma’a ta bayar da umarnin tsare wani manomi mai shekaru 50, Aka Anyam, a gidan gyaran hali, bisa zarginsa da kashe wani Gabriel Ayia.
Mista Annyam, wanda dan asalin garin Tse-Norum ne, a karamar hukumar Gwer-East ta jihar Benue, an tuhume shi da laifin hada baki, wanda ya haddasa mummunan rauni da kuma kisa.
Lauyan masu shigar da kara, Godwin Ato, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ga kwamishinan ‘yan sandan Benue ta wata kara a ranar 22 ga watan Afrilu.
Mista Ato ya ce, Bello Weren Esq ne ya rubuta koken a madadin wanda ya kai karar, Godwin Ayia, da ke zaune daura da gidan Rediyon Benue, Makurdi, kan iyalan Awolowo Norum na Tse-Norum, karamar hukumar Gwer-West ta jihar Benue.
Mai shigar da karar ya yi zargin cewa, wani lokaci a shekarar 2014, danginsa sun samu sabani da dangin Awolowo Norum.
Ya ce, daga nan ne aka kai rahoton lamarin ga sarakunan gargajiyar kasar, kuma suna ta bincike har zuwa yau. In ji People Gazzete.
Sai dai ya ce, bayan wani lokaci sai ‘yan uwan Awolowo suka shiga tashin hankali suka fara kai wa ‘yan uwansa hari.
Mai shigar da karar ya ce ba shi da wani zabi illa ya kai rahoton lamarin a hedikwatar ’yan sandan yankin da ke Makurdi a ranar 11 ga watan Maris kuma an aike da ‘yan sanda hudu tare da shi domin kamo maharan.
Ya kuma ce, a lokacin da ya isa Tse-Norum, ’yan gidan Awolowo 16 ne suka kai masa hari tare da ‘yan sanda tare da yi masa rauni a ka.
Mai shigar da karar ya ci gaba da cewa, a ranar 13 ga Afrilu, wadannan mutane sun kai wa dan uwansa, Jibrilu hari a gonarsa, inda suka yi masa duka tare da yi masa yanka har lahira.
Mai gabatar da kara ya kara da cewa tun da farko an kama mutane biyar aka gurfanar da su a gaban kuliya yayin da wanda ake zargin wanda ke boye a lokacin an kama shi. Sai dai Mista Ato ya ce har yanzu akwai sauran da dama.
Lauyan mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da tanadin sashe na 97, 248 da 222 na dokokin Penal Code na Benue, 2004.
Babban Alkalin Kotun, Vincent Kor, bai dauki karar wanda ake zargin ba na neman hurumin hukumta, kuma ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 29 ga watan Agusta, domin karin bayani.