Wata babbar kotun tarayya da ke Jos, babban birnin jihar Filato, ta yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Ochekpe, hukuncin daurin shekara shida a gidan yari.
Ochekpe ta kasance minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
An gurfanar da ita ne tare da wasu mutane biyu da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar a shekarar 2018 bisa zargin karbar Naira miliyan 450 daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur a shekarar 2015.
Raymond Dabo, tsohon shugaban riko na PDP a Filato, da Leo Jatau, jagoran yakin neman zaben Goodluck Johnathan a jihar a shekarar 2015, su ne sauran mutane biyun da aka yanke wa hukuncin.