Wata kotu a Peru ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Alejandro Toledo, hukuncin ɗaurin shekara ashirin da wata shida a gidan yari bisa samunsa da laifin almundahana da halasta kuɗaɗen haram.
Masu gabatar da ƙara sun ce ya karɓi fiye da dala miliyan 30 a matsayin cin hanci daga wani kamfanin gine-gine na Brazil wanda aka ba shi kwangilar gina titi a kudancin Peru.
Babban mai gabatar da kara na ƙasar ta Peru, Jose Domingo Perez, ya ce, wannan hukunci ne mai cike da tarihi, inda ya ƙara da cewa sako ne na cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka a ƙasar.
Mista Toledo mai shekara 77 ya yi mulki ne daga shekarar 2001 zuwa 2006.