fidelitybank

Kotu ta ɗaure mutumin da ya yi ƙarya da iyalin Buhari

Date:

Wata kotun majistare a Minna da ke jihar Neja, ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin ɗauri na shekara guda bisa zargin damfarar surukarsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Malam Gambo ya riƙa shaida wa surukarsa cewar yana shirya aure tsakaninta da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Surukar tasa, wadda bazawara ce ta garzaya kotu ne tare da koken cewa surukin nata ya yi mata wala-wala bayan karɓar kuɗin da suka kai naira miliyan biyar daga hannunta da sunan zai haɗa aure tsakaninta da tsohon shugaban ƙasar.

Ta shaida wa kotu cewa wata rana Gambo ya kai mata naira 100,000 a matsayin sadakinta, da huhun goro ɗaya da kuma soyayyiyar kaza da nufin cewa kyauta ce daga tsohon shugaban ƙasar, bayan ya yi mata ƙaryar ɗaura auren.

Ta ce a matsayinta na Amariya, ta yi ta dakon sabon angon nata ya zo ya ɗauketa.

Yayin da ba ta ganshi ba ne ya yanke shawarar kai surukin nata gaban kotun domin ta shiga tsakaninsu.

Alƙalin kotun, mai shari’a Ibrahim Musa Zago, ya ɗaure surukin nata wata 12 a gidan yarin, da zaɓin tarar naira 100,000, saboda samunsa da laifin cuta, laifin da ya saɓa da sashe na 322 na kundin final cod.

Haka kuma kotun ta umarci Malam Gambo ya biya surukar tasa naira miliyan biyu a matsayin diyya.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp