Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano karkashin mai shariʼa Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa wani matashi Abdullahi Nasir Kawo, hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari tare da biyan Ramkon 2,245,000.
An zargi matashin da shiga wani gidan kwanan dalibai mata da tsakar dare a unguwar Badawa, inda ya kwace musu wayoyi da kudade.
Kotu ta umarci ya biya kudin ne na jimillar wayoyi da kudaden da ya kwacewa daliban.
Mai Shariʼa Sarki Yola ya shawarci matashin da ya zama mutumin kirki bayan kammala zamansa a gidan gyaran hali.