Mai shari’a Agatha Okeke na babbar kotun Tarayya a Uyo, ta yanke hukuncin daurin shekara 235 kan Scales Olatunji.
An yankewa Olatunji wannan hukuncin ne bayan samun sa da laifin damfara ta intanet da halasta kudaden haramu.
Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa ce ta gabatar da shi gaban kotu.
A Yulin 2019 aka kama Olatunji tare da tuhumarsa da laifuka 45 da suka hada da basaja da sunan mutane da yaudara da dai saraunsu.
Olatunji dai da fari ya musanta aikata laifukansa, kafin daga bisa bayan gabatar da hujojji da bincike aka tabbatar da laifinsa.