Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu daga ranar Alhamis 26 ga watan Mayu zuwa 28 ga watan Yuni 2022.
Hakan na nufin zaman-a-gida da aka shirya yi a ranar Alhamis ba zai kara kasancewa a Kudu maso Gabas ba.
Lauyan IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya bayyana hakan a ranar Laraba a wata sanarwa.