Babbar kotun birnin Tarayya, ta ɗage sauraron ƙarar halasta kuɗin haram da aka shigar kan ma’aikatan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance zuwa ranar 17 ga watan Mayu.
An sanya ranar zaman shari’ar yau Alhamis sai dai a yanzu, an sake dage shari’ar.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Binance da ma’aikatanta biyu, Tigran Gambarayan da Nadeem Anjarwalla da laifin halasta kuɗin haram da ya kai dala miliyan 35.4.
Lauyan Gambarayan ya shaida wa kotu cewa, ba a bai wa wanda yake karewa takardun kotu ba, domin haka ya roƙi kotu ta jinkirta ƙarar.
Ita ma hukumar tattara haraji ta kasa na tuhumar Binance da ma’aikatan na ta da laifuka biyar da suka shafi kauce wa biyan haraji.
Tigran Gambarayan, wanda ɗan Amurka ne, ya musanta zargin tuhume-tuhumen da ake yi masa, yayin da har yanzu ake neman abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla ruwa a jallo, bayan ya tsere daga gidan gyaran hali a watan Maris.
Gambarayan, mai shekara 39 zai ci gaba da zama a tsare, har sai ranar 17 ga watan Mayu da za a ci gaba da zaman shari’ar.
Kotu ta ɗage shari’ar Binance da EFCC
Date: