fidelitybank

Kotu ta ɗage shari’ar ɗan awaren Biafara Nnamdi Kanu

Date:

Jagoran haramtacciyar ƙungiyar ‘yan’aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB), ya sake bayyana a gaban babbar kotun tarayya yau Juma’a a Abuja babban birnin Najeriya.

Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyinsa Aloy Ejimakor ya ce kotun ƙarƙashin Mai Shari’a James Kolawole ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 29 ga watan Afrilu da kuma 2 da 6 ga watan Mayu na 2025.

Ci gaba da shari’ar ta Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan Alƙaliyar Alƙalai Kudirat Kekere-Ekunnyefere ta saka Mai Shari’a James Kolawole Omotoshi a matsayin sabon alƙalin da zai saurari shari’ar bayan Kanu ya yi ƙorafi kan Mai Shari’a Binta Nyako.

Ana yi hasashen za a yi bitar tuhuma bakwai da gwamatin Najeriya ke yi wa Kanu yayin ci gaba da shari’ar, waɗanda suka jiɓanci tayar da fitina da kuma ta’addanci.

A watan Disamban 2023 ne Kotun Ƙoli ta umarci Kanu ya koma babbar kotun ta tarayya domin kare tuhumar da ake yi masa bayan Binta Nyako ta yi watsi da takwas cikin 15 da gwamnati ta gabatar a 2021.

Gwamnatin Najeriya ta kai Kanu kotu ne bayan kama shi a wata ƙasar waje a 2021, kuma har yanzu mambobin ƙungiyarsa da gwamnati ta haramta na ci gaba da neman ɓallewa daga Najeiriya domin kafa ƙasar Biafra.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp