Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar da hukuncin kotun tarayya na cewa fiye da motoci 40 da aka kwato daga gidan tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, mallakin gwamnatin jiha ne.
Alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A.M. Talba sun yi watsi da ƙarar da Matawalle ya shigar, inda suka bayyana cewa bai gabatar da kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa shine mai mallakar motocin ba.
Lamarin ya samo asali ne tun watan Yuni a shekarar 2023, lokacin da gwamnatin Zamfara ta bai wa tsohon gwamnan da mataimakinsa kwanaki biyar su dawo da motocin gwamnati da suka kwashe bayan sauka daga mulki, amma suka ƙi. Daga bisani kotu ta bayar da izinin jami’an ‘yan sanda su kwato su.
Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya ce wannan hukunci ya tabbatar da cewa motocin za su ci gaba da kasancewa mallakin gwamnatin Zamfara, tare da bai wa ‘yan sanda damar cigaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da masu laifi.