Kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Benue ta bayyana Sanata Gabriel Suswam na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan da aka yi a mazabar Benuwe ta Arewa maso Gabas a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Suswam ya doke Emmanuel Udende na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kotun, inda aka yi masa turereniya a ranar Juma’a, bayan yanke hukuncin da ya dauki sama da sa’o’i uku.


