Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amince wa da buƙatar hana gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas kashe kuɗaɗen gwamnati yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar da majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule ta shigar.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Emeka Nwite ya ƙi amince wa da umarnin da aka nema.
Sai dai ya umarci masu shigar da ƙara da su sanar da waɗanda ake ƙara game da lamarin.
Za a ci gaba da shari’ar ne a ranar 7 ga watan Agusta inda kotu za ta saurari ƙarar da aka shigar.
Wadanda ake tuhuma sun hada da Gwamna Fubara da Akanta-Janar na Jihar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar (RSIEC) da Alƙalin Alkalan Jihar Justice S.C. Amadi.


