Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC, ta samu daurin shekaru bakwai ga wani jami’in gwamnati a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mista Amdii Monday Gideon, bisa samunsa da hannu a badakalar bayar da aiki.
A karar da ICPC ta shigar a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja mai lamba 17 a Gwagwalada, ana tuhumar wanda ake tuhuma da neman kudi Naira 250,000 tare da karbar kudi Naira 162,500 daga hannun mai bukata tare da alkawarin samo mai aiki a Hukumar Ma’aikata ta Tarayya.
Wanda aka azabtar ya kai kararsa ga ICPC bayan wanda aka yankewa laifin ya kasa samun aikin da aka ce, ya ki mayar da kudinsa.