fidelitybank

Kotu ta ɗaure jagororin zanga-zangar jihar Katsina

Date:

Wata kotu a jihar Katsina ta tura 7 daga cikin jagororin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar, gidan yari tsawon wata ɗaya.

Wani makusancin biyu daga cikin jagororin ya shead wa BBC cewa, a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar ta gurfanar da Kwamared Habibu Ruma da Kwamared Kabir Shehu ‘Yanɗaki da kuma wasu mutum biyar a gaban kotun majistare a birnin Katsina, inda ta tuhume su da laifukan da suka haɗa da tarzoma da sata da kuma ɓarnata kayan gwamnati.

Bayan an karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, ”sai kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 11 ga wata mai zuwa, Satumba, 2024 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare mutanen bakwai a gidan kaso, zaman waƙafi.

An gudanar da zanga-zanga ta gama-gari daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024 zuwa 10 ga watan na Agusta 2024, saboda matsaloli da suke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da tsadar rayuwa da rashin tsaro musammana a arewacin da neman shugabanci na gari.

Sai dai yayin da zanga-zangar ta kasance cikin lumana a wasu jihohin, a wasu kuwa ta rikiɗe ta zama tarzoma inda aka riƙa sace-sace da ɓarnata kayan gwamnati da na ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikum mutane.

Tarzomar ta kuma yi sanadin kashe mutane da jikkata wasu da dama.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp