Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dage shari’a kan karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kan gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da mataimakinsa Farfesa Ivana Esu.
Mai shari’a Taiwo Taiwo, wanda da farko ya sanya ranar 25 ga watan Maris don yanke hukunci kan karar, a yanzu ya dage yanke hukunci a karar zuwa ranar Laraba 6 ga Afrilu.
Sai dai ya sanya ranar Alhamis 7 ga watan Afrilu domin yanke hukunci bayan lauyoyin da ke wakiltar bangarorin da ke kara sun yi jawabi ga kotun a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta Enugu ta yanke kan sauya shekar Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi.
Wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Emmanuel Ukala, shi ne ya wakilci PDP yayin da wani SAN Mike Ozekhome ya wakilci Gwamna Ayade.
A cikin jawabinsa, Ukala ya dage kan cewa abin da ake magana a kai, da batutuwan da aka gabatar don tantancewa, da kuma tafsirin wasu tanade-tanade na kundin tsarin mulkin kasar nan a shari’ar Umahi da Ayade, sun sha bamban.
Ya ce, addu’ar Umahi a babbar kotun Abakiliki ta sha bamban da abin da PDP ke nema a babbar kotun tarayya da ke Abuja.