Wata babbar kotun jihar Ribas da ke zamanta a birnin Fatakwal ta tsare wasu mutum hudu a gidan yari, saboda da zargin fashi da makami a gidan matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan.
Ana tuhumar matasan da laifuka biyar da suka hadar da hadin baki, da sata, da fashi da makami, da kuma yunkurin kisan kai.
Ana dai zargi mutanen hudu da kutsawa gidan matar tsohon shugaban kasar wanda ke unguwar GRA a birnin Fatakwal, inda suka saci kayayyaki na miliyoyin nairori.
Zargin da matasan hudu duka suka musanta bayan karonto musu tuhumar a gaban gotu.