fidelitybank

Kotu na neman dan Burtaniya ruwa a jallo

Date:

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umarnin kamo wani dan Burtaniya, James Nolan saboda ya keta sharuddan beli.

Mai shari’ah Ahmed Mohammed ne ya ba da umarnin bayan James Nolan wanda darakta ne a kamfanin Process and Industrial Development Limited (P&ID) ya gaza bayyana a gaban kotu.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta shigar da James kara tare da kamfanin Lurgi Consult Limited da sauran wasu, a wata shari’a da ta shafi halasta kudin haram kimanin dala biliyan 9.6.

Da yanke ba da hukunci, Mai shari’ah Ahmed Mohammed ya ce James ya karya sharuddan belin da kotu ta ba shi, don haka kotu ta soke belin kuma ta fitar da sammaci don a kamo shi, duk inda ya shiga.

Tashar talbijin ta Channels ruwaito alkalin na kuma umarci mutumin da ya tsayawa James Nolan ya bayyana a gaban kotu lokacin zaman kotu na gaba, don ya yi mata bayani a kan dalilin da ya sa kotu ba za ta karbe takardun lamuni da ya ajiye a kotu ba.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp