Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jaddada matsayarsa cewa, kotu ce kaɗai za ta tantance matsayin jagoran ‘yan ƙungiyar aware masu neman kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu.
Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma’a yayin ganawarsa da shugabannin ƙabilar Igbo a Jihar Ebonyi bayan jagororin sun roƙe shi ya saki Kanu, wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a a gaban kotu ka zargin tayar da hankali da raba kan ‘yan ƙasa.
“Na saurari roƙon dattijai da shugabannin gargajiya daban-daban da kyau game da batutuwa,” in ji Buhari. “Kuma kamar yadda na faɗa a baya, wannan lamarin zai ci gaba da kasancewa a hannun kotu, inda za a ba shi kulawar da ta dace.”
Ya ƙara da cewa: “Damuwata ita ce fararen hularmu waɗanda da ma can rayuwarsu na cikin ƙunci kuma suke so su fita kawai don su nemi abin da za su ci abinci.”