Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo, ya ce, kotun koli ba za ta samu shugaban kasa Bola Tinubu da laifin yin bogi ba.
Keyamo ya bayyana hakan ne a wani dogon sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
Da yake jawabi a kan cece-kucen da suka taso a wannan makon, bayan da Jami’ar Jihar Chicago (CSU) ta bayyana bayanan da Tinubu ya samu a fannin ilimi, Keyamo ya dage cewa “ba za ka iya yin zargin ko tabbatar da jabu ba sai dai wanda ake zargin ya yi takardar ya musanta sahihancinsa”.