Koriya ta Kudu ta sanya sabbin takunkumai a kan wasu daidaikun mutane, da hukumomi da ke da alaka da shirin makamai na Koriya ta Arewa, sakamakon kaddamar da manyan makamai masu linzamin da makwabciyar tata ke yi akai-akai.
Ma’aikatar harkokin waje ta Koriya ta Kudun ta ce mutane takwas da hukumomi bakwai da abin ya shafa, sun hada da jami’ai a cibiyoyin kudi da ke da alaka da shirin nukiliya da kuma na makamai masu linzami na kasar ta Koriya ta Arewa.
Wasu kuma su ne wadanda ke da hannu wajen haramtacciyar safara ta jiragen ruwa ta kayan Koriya ta Arewa da aka sanya wa takunkumi.
Tun da farko Amurka ma ta sanya wa wasu manyan jami’ai na Koriya ta Arewar uku takunkumi, wadanda ta ce suna da hannu kai tsaye a kera makamai.